Labaran ƙasa
Majalissar Dattijai Tayi Sammacin Ministar Kudi
Majalissar Dattijai tayi sammacin Ministan kudin tarayyar Najeriya Zainab Shamsuna Ahmad, Dan tayi musu bayanin akan kudi Kimanin Naira Biliyan 206 da aka sa acikin kasafin kudin shekara 2023 na ma’akatar Jin kai da kula da walwalar Al’umma.
Kwamitin Ayyuka na musamman na majalissar Dattijan sun bukaci Ministan da tazo tayi musu bayani, akan wadannan makudan kudaden da aka sa duk da halin karancin haraji da matsin tattalin Arziki da Kasar ke fama da shi a wannan lokacin.
Jaridar Premium Times ta ruwaito cews bukatar gayyatar ministan ta samo asali ne, a lokacin kare kasafin kudin ma’aikatar jin kai da kula da walwalar Al’umma.
Biyo bayan kasa sahihin bayani da ministar ma”aikatar Sadiya Umar Faruq tayi akan kudaden, Sadiya ta bayyana cewa bata san ta yaya akayi ma’akatar kudin ta saka kudaden a cikin kasafin kudin ma’akatarta na shekara mai kamawa ba.
Ta bayyana cewa kuma, ma’akatarta ta bukaci wasu kudade a wannan shekarar da muke ciki Dan yin wasu Ayyuka a hukumar cigaban yankin Arewa maso Gabas.
Saidai ta bayyana cewa bata saki kudaden ba a lokacin, amma yanzu tayi mamakin ganin kudin har ninki goma acikin kasafin kudin ma’akatarta na shekara mai zuwa.
Memba acikin kwamitin sauraran bayanan kasafin kudin Elisha Abbo yayi ikirarin cewa, akwai bukatar su gayyato Minista Zainab Dan tayi musu bayanin yadda aka sanya kudaden.
Inda yace sun gano kudi kimanin Biliyan 301 wanda za’a biyasu ta hanyar ciyo bashi mabanbanta, kuma sun tambayi ministan da tayi musu bayani akan ayyukan da za’ayi dasu.
Saidai ya kara da cewa, Sadiya ta gaza yi musu jawabi akai, tace bata san dasu ba saidai a tambayi ministar kudi Zainab Ahmad Shamsuna.
Labaran ƙasa
Ba Mu Ƙayyade Shekarun Rubuta Jarrabawar WAEC Da NECO Ba – Gwamnatin Tarayya
Ƙaramin ministan ilimi a Najeriya Dakta Yusuf Sununu ya ce gwamnatin tarayya ba ta hana dalibai yan ƙasa da shekara 18 rubuta jarrabawa ba.
Ministan ya ce gwamnatin ba ta hana dalibai rubuta jarrabawar kammala sakadire ba
Dakta Sununu ya bayyana haka ne yau yayin wani taro a Abuja.
A cewarsa, mutane basu fahimci bayanin ministan ilimi Farfesa Tahir Mamman ba.
Ya ce sun kadu da su ka samu labarin cewar ana baiwa dalibai yan shakara 10, 11 da 12 gurbin karatu a manyan makarantu.
Duk da cewar akwai yan baiwa da za su iya kararu a manyan makarantun, sai dai ya c ba su da yawa.
Dakta Sununu ya ce gwamnati ba ta hana ɗalibai ƴan ƙasa da shekara 18 rubuta jarrabawar WAEC da NECO a ƙasar ba
Idan za a iya tunawa a kwanakin baya an kai ruwa rana kan bai wa dalibai yan ƙasa da shekara 18 gurbin karatu a jami’a da sauran manyan makarantu.
Labaran ƙasa
Tsananin Da Najeriya Ke Ciki Cigaba Ne A Gareta
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce tsauraran matakai masu wahala da ake dauka a ƙasar zai taimaka wajen cigaban kasar ne.
Tinubu na wannan jawabi ne a ƙasar China wanda ya ce ƙarin farashin da aka samu zai taimaka wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.
Tinubu ya ce matakan da ake ɗauka na farfado da ƙasar.
Tinubu na wannan jawabi ne sakamakon ƙarin farashin man fetur da aka samu a ƙasar wanda al’umma ke kokawa.
A jihar Kwara masu ababen hawa sun yi zanga-zanga wanda hakan ya sanya matafiya yin cirko-cirko.
Sai dai gwamnatin kasar na cewar za a kawo karshen wahalarsa cikin ƙarshen mako da za mu shiga.
Labaran ƙasa
Mutanen Da Za Su Ci Gajiyar Garaɓasar Shinkafar Gwamnati
Gwamnatin tarayya a Najeriya ta ce mutanen da su ke da lambar zama ɗan ƙasa ta NIN ne kaɗai zasu amfana da shinkafar da za ta siyar naira 40,000 buhu guda
Ministan harkokin noma Abubakar Kyari ne ya bayyana haka yayin da yake kaddamar da tsarin wanda aka karyar da farashin don saukakawa yan kasar.
Kyari wanda ya wakilci shugaba Bola Tinubu ya ce za a siyarwa da duk magidanci guda buhun shinkafa.
Sannan buhu guda mai nauyin kilo 50 za a siyar naira 40,000.
Ministan ya ce an fara siyar da shinkafar daga jiya Alhamis kuma waɗanda ke da lambar zama ɗan ƙasa ne kaɗai za su ci gajiyar tsarin.
Ministan ya alakanta tsadar kayan abinci da yunwa da ake ciki da annobar korona da kuma yaki tsakanin Rasha da Ukraine.
Sai dai wadanda ke aikin gwamnati su ke tsarin biyan albashi za a siyarwa da shinkafar.
-
Labarai7 months ago
Mafi Karancin Sadaki A Najeriya Ya Koma Dubu 99,241
-
Mu shaƙata2 years ago
Kun San Ma’anar Kalmar Chiza Dani? Waƙar Da Ke Tashe A Kwanakin Nan?
-
Labaran ƙetare5 years ago
Wajibi ne duk wani namiji ya Auri mata Biyar ko a ɗaure shi a gidan yari— Sarkin Swaziland
-
Al'ada5 years ago
Fahimta ta a kan matsalar aure a ƙasar Hausa
-
Labarai5 years ago
Ba kwaya ƴan sandan kano suka kama ba, babu sinadarin maye a cikin maganin – NAFDAC
-
Addini4 years ago
Lokutan da ake saurin karɓar addu’a
-
Lafiya6 years ago
Menene Genotype ? Amfanin yinsa kafin Aure – Mujallar Matashiya
-
Mata adon gari5 years ago
Sinadarin gyaran gashi – Adon Gari