Ministar Tallafi da jin kan al’umma, Sadiya Farouq, ta tuhumi Ministar Kudi, Zainab Ahmed, da sanya kudi N206bn cikin kasafin kudin ma’aikatar na 2023.

Hajiya Sadiya ta bayyana hakan ne ga kwamitin majalisar dattawa ranar Litinin inda ta tafi munakasha kan kasafin kudin ma’aikata na 2023.

Tace akwai wasu kudade na hukumar cigaban yankin Arewa maso yamma da aka sanya a kasafin kudin 2022 amma ba’a basu kudaden ba, yanzu kuma an sake sanya kudin cikin na 2023 har ninkin ba niki.

An fara takkadama ne lokacin Sanata Elisha Abbo, ya tuhumci Sadiya da cusa kudi N206bn cikin kasafin kudi, riwayar AIT.

Sadiya ta ce ba’a basu kudaden ba, yanzu kuma suna ganin ya ninku kusan ninki 10, zasu tambayi ma’aikatar kudi tayi musu bayani kan dalilin saka kudin ciki duk da cewa ba’a fitar ba a bara.

Sai dai kuma Sanata Abbo ya bayyana mamakinsa bisa jawabin Ministar.

Ya ce ta wani dalili za’a rika karban basussukan kudade da sunan ana amfani dasu wajen aiki alhalin ba’a amfani da su.

Shugaban kwamitin, Sanata Yusuf Yusuf ya bukaci ayi sammacin Ministar kudi tayi bayanin yadda ta cusa N206bn cikin kasafin kudin 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: