Kungiyar malaman jami’o’i watau ASUU, suna barazanar tsallake zangon karatun da aka samu a tangarda a dalilin dogon yajin-aikin da aka yi.

Manema labarai sun rahoto cewa idan har gwamnatin tarayya ta ki biyan malaman jami’a albashinsu, za su tsallake zangon karatun da ya shude.

Wasu malaman jami’ar UNIPORT ta jihar Ribas sun bayyana cewa ba za ta yiwu a hana su kudinsu ba tun da dai suna biyan bashin karatun da ya wuce.

Malaman sun ce a halin yanzu sun gwamutsa karatuttukan zango mai-ci da wanda ya wuce basuyi ba.

Gwamnatin tarayya tace ba za ta biya ‘yan ASUU kudin aikin da ba suyi ba, amma malaman jami’o’in gwamnati sun ce ba za su yarda da wannan tsari ba.

A cewar ‘ya ‘yan kungiyar na ASUU, ana biyan malamin jami’a albashinsu ne duk wata, ba jinga ake yi da shi na daidai gwagwardon ayyukan da suka yi ba

Leave a Reply

%d bloggers like this: