Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa a Najeriya aka buga sabbin takardun kudade na Naira 200, Naira 500 da kuma Naira 1000 wadanda aka kaddamar a jiya Laraba, a babban birnin tarayya Abuja, kuma Kamfanin buga Muhimman Takardu na Kasa (NSPM) ne ya buga takardun kudin.

A jawabinsa yayin kaddamar da sabbin takardun kudin, Buhari ya ce an kara inganta matakan tsaron da ke jikinsu ta yadda buga jabinsu zai yi wuya, kuma wannan na daga cikin dalilan da su ka sa ya amince da bukatar Babban Bankin Najeriya (CBN) na sauya fasalin takardun kudin.
Ya kuma jinjina wa Gwamnan CBN, Godwin Emefiele da mataimakansa da suka bukaci tabbatar da sauyin kudaden, da kuma shugabannin kamfanin NSPM da ma’aikatansu, bisa aikin da suka yi ka’in-da-na’in tare da CBN wajen tabbatar da kammala aikin cikin kankanin lokaci.

A cewarsa, tsarin kudade na duniya ya tanadi a sabunta takardun kudin kasa bayan kowacce shekara biyar zuwa takwas, amma yanzu kusan shekara 20 ke nan rabon da a yi hakan a Najeriya.

Don haka ya ce lokacin sauya takardun kudin ya dade da yi, amma ba a yi ba.
Ya kara da cewa manufar sauye-sauyen sun hada da Inganta tsaron kudi, hana buga jabu, kayyade takardun kudi da ke yawo a hannun jama’a tare da rage kudaden da ake kashewa wajen kula da takardun kudade.
Buhari ya ce kamar yadda aka sani dokokin cikin gida musamman dokar CBN ta shekarar 2007 ta bai wa babban bankin ikon bayarwa da kuma sauya takardun Naira A kan haka ne a farkon wannan shekara Gwamnan CBN ya gabatar masa da wannan bukata.
Bayan nazarin dalilai da hujjojin da suka bayar yasa Shugaba Buhari ya amince da bukatar.