Majalisar wakilan Rasha ta amince da sabuwar dokar haramta yada farfaganda da ke goyon bayan auren jinsi a fadin kasar.

Sabuwar dokar wadda aka kada wa kuri’a ba tare da hamayya ba, majalisar ta tsaya kai da fata game da matsayarta na haramta duk wata alakar auratayya da ta sabawa yadda dan adam ya gada tsawon shekaru a ban kasa.

Da yake jawabi game da sabuwa dokar kakakin majalisar wakilan ta Rasha Vyacheslav Volodi, ya ce akwai hukunci mai tsauri akan duk wanda aka samu da laifi wanda ya saba da halittar dan adam.

Majalisar ta Rasha cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Telegram, ta ce sabuwar dokar zata kange al’ummar kasar musamman masu tasowa a nan gaba daga mummunar akidar wadda Amurka da kasashen Turai ke son karfafawa a duniya.

Dokar dai na bukatar goyon bayan majalisar dattijai da kuma sanya hannun shugaba Vladimir Putin gabanin fara aiki da ita tare da hukunta wadanda aka samu da dabi’ar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: