Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’anati a Najeriya EFCC ya bayyana cewa suna sane da wasu gwamnoni Uku da suke yinkurin biyan albashi ga ma’aikatan gwamnatin hannu da hannu.

Bawa ya bayyana haka a jiya cikin wata hira da jaridar Daily trust su ka yi da shi.

Cikin gwamnoni Ukun da bai fadi sunan su ba amma ya ce, biyu na Arewacin Najeriya Daya kuma kudanci.

Sannan ya ci gaba da cewa sun samu masaniyar cewa gwamnoni Ukun sun ajiye wasu makudan kudade a gidajen su wadanda suke so su shigar da su asusu tun bayan ayyana chanja samfurin kudaden Najeriya da babban banki CBN yayi sakamakon faduwar tattalin arzikin kasar.

Abdurasheed bawa ya ce ba za su bari haka ta faru ba saboda hakan babban laifi ne, tun da tun farko ana biyan kudi ta asusu sai yanzu da aka yi maganar sauyin kudi sai wasu gwammnoni su ce za su biya albashi ba ta banki ba.

Sannan ya ce kuma suna ci gaba da sanya Ido akan masu yin canjin dala saboda itama ta na barazana ga tattalin arzikin kasa.

Sai dai da aka tambayeshi ko za su gayyaci gwamnonin ofishin su domin amsa tambayoyi? ya ce ba za su yi haka ba amma ba za su bari a biya albashi ba in ba yadda aka saba ba.

Kuma kai’dar ita ce bukata ta mutum daya shi ne miliyan biyar kamfani miliyan Goma

A ranar 26 ga watan Oktoba babban Banki na kasa wato CBN ya bayyana za a canja fasalin kudi daga 1000 500 200 Sakamakon tsadar rayuwa da faduwar ita kanta nairar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: