Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta gina sabuwar tashar hasken wutar lantarki a jihar Borno wadda za ta dinga amfani da gas.

Babban ministan wutar lantarki na kasa Abubakar Aliyu shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a ofishinsa dake babban birnin tarayya Abuja a jiya Juma a.

Aliyu ya ce ya baiwa babban kamfanin Mai na kasa NNPC lasisin gudanar da fara aikin kuma za dinga amfani ne da iskar Gas.

Ya ce tuni an fara aikin ginawa batare da bata lokaci ba ta yadda za a magance matsalar cikin kankanin lokaci.

Sannan tashar wadda za a yi ta a babban birnin jihar Borno wato Maiduguri za a samu wutar lantarki tsawon megawatt 50 a fadin garin.

Injiniya Abdullahi Aliyu ya ci gaba da cewa za a yi aiki ne Sakamakon karancin hasken lantarki da ake samu a fadin wasu kananan hukumomi saboda zargin da ake yiwa yan boko haram da lalata wasu kayan aiki.

Sannan ya ci gaba da cewa gwamnatin tarayya ta dukufa wajen magance matsalar hasken lantarki a kasar kuma ana nan ana ci gaba da baiwa kamfanunuwa da za su bayar da gudunmawa dama domin inganta harkar lantarki a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: