Akalla mutane 211 ne suka rasa rayukansu a cikin watanni goma da su ka gabata sakamakon hatsari a jihar Kwara a cewar hukumar kiyaye hadura ta kasa.

Babban kwamandan hukumar kiyaye haddura ta kasa Frederick Ade Odigan shi ne ya bayyana haka a yau Asabar a wani taron don fadakar da jama’a game da kiyaye tuki.

Odigan ya ce mutane 211 ne su ka mutu bayan aukuwar haddura a jihar Kwara a manyan tituna daban daban na jihar.

Ya ci gaba da cewa akalla an samu hatsari guda 284 daga watan Janairu zuwa watan Oktoba 2022, kuma ababen hawa 477 ne suka lalace a lokacin hadarin.

Sannan mutane 933 ne suka samu raunuka maza 309 da kuma mata 1,679 da kananan yara 99 a ciki.

Jami’in ya kara da cewa alumma su daina wulakanta jami’an hukumar kiyaye hadura yayin da suke bakin aikn su domin hakan dakile kasa ne.

Daga karshe yayi roko ga jama’a da su dinga bin doka da kaidoji na tuki kuma su daina amfani da tsohowar taya da daukar kayan da ya wuce mizani a yayin tuki.

Taron wanda aka yi a babban birnin jihar Kwara Ilori ya samu halartar manyan masu rike da sarautun gargajiya da sauran mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: