Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa, ‘yan ta’adda sun kashe kimanin mutane 15 a wasu mabanbantan hare-hare da aka kai a garuruwan Giwa, Birnin Gwari da kuma karamar hukumar Kajuru na Jihar.

Kwamishinan Tsaro da Al’amuran cikin gida Samuel Aruwan a jiya Juma’a ya bayyana cewa, kashe-kashen ya faru ne a Rafin Sarki, Hibiya da kuma Damari da suke yankin kananan hukumomin.
Jaridar Premium Times ta ruwaito Aruwan ya bayyana cewa, hukumomin tsaro su suka sanar da gwamnatin jihar faruwar lamarin.

Ya kuma bayyana cewa Gwamnan Jihar ta Kaduna Nasir El-Rufa’i ya bayyana takaicinsa ga faruwar lamarin, ya kuma mika sakon jaje da ta’aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Sannan kuma Gwamnan yayi Addu’ar samun sauki ga wadanda suka jikkata a lokacin faruwar hare-haren.
Aruwan ya kuma bayyana cewa, Gwamnan ya bukaci jami’ai da hukumomin tsaro da su shiga cikin lamarin da gaggawa, Dan gudun faruwar irin hakan anan gaba.