Shugaban jamiyar APC na jihar kano Abdullahi Abbas ya musanta zarge_zargen da ake masa na cewa yana yin kalaman tada hargitsi a lakacin taron siyasa.

Abdullahi Abbas ya bayyana haka a wata hira da BBC ta yi da shi inda ya ce yan adawa ne kawai su ke canja magana amma ba ya nufin tada hargitsi a cikin kalaman na sa.

Abbass Wanda ake zargi da yin kalaman tada hargitsi kamar ko da tsiya tsiya ko ana ha maza ko mata da ko me za ai kuma ko mai zaifaru sai sun ci zabe.

Sai dai shugaban jamiyar na APC na kanon ya ce ba haka yake nufi ba a bayanin na sa, ya na nufin tsiya tsiya irin ta kuri a da za su kada yayin zabe.

Abdullahi ya ci gabada cewa wadanda kalamai ya Dade ya na yin don tun shekarar 2019 kuma ko a lokacin bu su kawo hargitsi ba kaga kuwa ba sa kawo matsala.

Sannan ya ce duk masu zarge zarge zargen sa akan Wadannan kalaman cewa kawai adawa ce irin ta siyasa amma su alumman jihar ai sun san kalaman ba sa tada hanakali ba ne shiya sa ma basa magana akan lamarin.

Ya kuma ce a wannan karon ba za su bari a yi musu irin ta da baya ba saboda an sha su sun warke don haka a wannan lokaci babu inconclusive a zabe domin falan Daya za su yi sun ci zabe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: