Gobara ta tashi a wata makarantar firamare ta kwana tare da murkushe ajujuwa 14 da wasu sauran ofishoshi a kano.

Lamarin ya faru ne jiya Lahadi a karamar hukumar Bagwai ta jihar kano.
Mai magana da yawun hukumar kashe Gobara ta kano Saminu Abdullahi shi ne ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce gobarar ta yiwa makarantar firamare illa sosai.

Ya ce sun samu Kiran waya wani mutum bisa tashin goborar a jiya da misalin karfe Daya na rana.

Ya ce da samun jin haka suka tura jamian su domin kawar da matsalar kuma an yi nan take .
Gobarar ta tashi ne a sakamakon wutar sola wadda ke cikin ofishin malamai.
Sai Goborar ta cinye ajujuwa 14 da kuma ofishoshin malamai 12 da bandakuna 21.
Saminu Abdullahi ya bai bayyana ko an samu asarar a yayin gobarar.