Rundunar Yan sanadan Najeriya ta umarci dukanin kwamishinoninta na jihohi da su tura jami ai domin baiwa hukumar zabe INEC kariya.

Babban sufetan na kasa Usman Alkali Baba shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a ta bakin Mai maganar da yawun hukumar ta yan sanda Olumoyiwa Adejobi a jiya Lahadi.

A cewarsa za a gudanar za a ranar biyu ga watan fabarairu 2023.

Alakali Baba ya ce sun umarci dukanin kwamishinonin Yan sanda da su tura jami ai ofishin hukumar zabe ta kasa INEC domin bayar da kariya ga hukumar.
Sannan ya ci ga ba da cewa za garfanar da duk Wanda aka samu da tada tarzoma kalaman karya da tsattsauran ra ayin siyasa don yin haka barazana ne ga damakwaradiyya a Najeriya.
Sannan ya ce za a yi tsarin wanda za a samu damar lalubo hanayar da ya da ce baiwa INEC kariya yayin zabe ya Kara Karatowa.
Sannan Usman Alkali Baba ya ce kuma ya zama dole jama a su taya su gurin tabbatar da wannan aikin domin yan sanda kadai baza su iya aikin su kadai ba .
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce ta gano wasu mutane 100 da su ke turawa yan kunguyar taaddanci kudade a fadin kasar.
Yayin da yake magana a wajen taron mai taken ba kudi ga dan ta’adda babban ministan harkokin ciki gida Rauf Arebesola ya bayyana haka ta bakin mai taimaka masa Abdulmalik Sulaiman a jiya Lahadi.
Rauf ya ce bayan binciken watanni 19 da suka gudanar sun samu nasarar kama mutane 100 wadanda suke taimakawa Yan ta’adda da kudade.
Ya ci gaba da cewa sun yi amfani da hukumar NFIU tare da takwarorinta na tsaro wajen gudanar da binciken.
Sannan ya ce mutanen 100 da suka gano sun fito ne daga kasashe Goma na duniiya.
Sannan ya ce sun kama mutane 48 daga ciki bayan shafe watanni ana binciken.
Sannan daga karshe minista Rauf Arebesola yayi kira ga gwamnati data kara walwalar mutane dalibai da kuma masu neman aikin yi domin dakile matsalar rashin tsaro a fadin kasa Najeriya.
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta Kama wani mutum da yayi yinkurin safarar ibilis a cikin takalmi zuwa kasar Saudiya.
An Kama Wanda ake zargin ne a ranar alamis din data gabata a cewar babban Jami in dake hulda da jama a na hukumar wato Femi BabaFemi.
Femi ya ce sun samu akalla hodar ibilis wadda ta kai kimanin kilo 400 wadda ya boye a cikin takalman sa ya na kokarin fita da su zuwa kasar Saudiya.
Ya ci gaba da cewa an Kama mutumin mai shekara 56 a duniiya mai suna Lawal Oyenuga a babban filin tashin jiragen sama na Murtala Mahammadu dake jihar Leges a kudancin Najeriya.
BabaFemi ya ce mutumin yayi yunkurin sanya hodar ibilis a cikin takalman sa ya shiga da su izuwa kasar Saudiya domin yin cinikayyar kwayoyi.
Sai dai Jami an su na hukumar ta NDLEA sun yi Nasarar Kama wanda ake zargin.
Daga karshe ya ce bayan kammala bincike za su mika wanda ake zargin zuwa kotu domin karbar hukunci.
Gobara ta tashi a wata makarantar firamare ta kwana tare da murkushe ajujuwa 14 da wasu sauran ofishoshi a kano.
Lamarin ya faru ne jiya Lahadi a karamar hukumar Bagwai ta jihar kano.
Mai magana da yawun hukumar kashe Gobara ta kano Saminu Abdullahi shi ne ya bayyana haka ga manema labarai inda ya ce gobarar ta yiwa makarantar firamare illa sosai.
Ya ce sun samu Kiran waya wani mutum bisa tashin goborar a jiya da misalin karfe Daya na rana.
Ya ce da samun jin haka suka tura jamian su domin kawar da matsalar kuma an yi nan take .
Gobarar ta tashi ne a sakamakon wutar sola wadda ke cikin ofishin malamai.
Sai Goborar ta cinye ajujuwa 14 da kuma ofishoshin malamai 12 da bandakuna 21.
Saminu Abdullahi ya bai bayyana ko an samu asarar a yayin gobarar.
Shugaban jamiyar APC na jihar kano Abdullahi Abbas ya musanta zarge_zargen da ake masa na cewa yana yin kalaman tada hargitsi a lakacin taron siyasa.
Abdullahi Abbas ya bayyana haka a wata hira da BBC ta yi da shi inda ya ce yan adawa ne kawai su ke canja magana amma ba ya nufin tada hargitsi a cikin kalaman na sa.
Abbass Wanda ake zargi da yin kalaman tada hargitsi kamar ko da tsiya tsiya ko ana ha maza ko mata da ko me za ai kuma ko mai zaifaru sai sun ci zabe.
Sai dai shugaban jamiyar na APC na kanon ya ce ba haka yake nufi ba a bayanin na sa, ya na nufin tsiya tsiya irin ta kuri a da za su kada yayin zabe.
Abdullahi ya ci gabada cewa wadanda kalamai ya Dade ya na yin don tun shekarar 2019 kuma ko a lokacin bu su kawo hargitsi ba kaga kuwa ba sa kawo matsala.
Sannan ya ce duk masu zarge zarge zargen sa akan Wadannan kalaman cewa kawai adawa ce irin ta siyasa amma su alumman jihar ai sun san kalaman ba sa tada hanakali ba ne shiya sa ma basa magana akan lamarin.
Ya kuma ce a wannan karon ba za su bari a yi musu irin ta da baya ba saboda an sha su sun warke don haka a wannan lokaci babu inconclusive a zabe domin falan Daya za su yi sun ci zabe.
Rundunar sojin Najeriya sun hallaka wasu daga yan ta dan Hudu a jihar kaduna.
Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Chukun a dajin tsohon Gayan a jihar kaduna.
Kwamishinan tsaron harkokin cikin gida Samuel Aruwan shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a jiya Lahadi.
Sojin sun hallaka yan bindigan ne a lokacin da suke maboyarsu a dajin tsohon Gayan a kaduna.
Samuel ya ci gaba da cewa a yayin bata kasihin an hallaka biyu daga ciki nan yayin aka kashe sauran daga baya.
Sannan ya ce sun samu bindinga Kirar AK47 da mashin da wasu sauran kayayyaki
Sannan ya ce mai girma gwamnan jihar kaduna ya ji dadi da jin wannan labarin sannan ya yabawa sojojin tare da cewa tsaro zai could gaba da gudana a jihar.