Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta Kama wani mutum da yayi yinkurin safarar ibilis a cikin takalmi zuwa kasar Saudiya.

An Kama Wanda ake zargin ne a ranar alamis din data gabata a cewar babban Jami in dake hulda da jama a na hukumar wato Femi BabaFemi.
Femi ya ce sun samu akalla hodar ibilis wadda ta kai kimanin kilo 400 wadda ya boye a cikin takalman sa ya na kokarin fita da su zuwa kasar Saudiya.

Ya ci gaba da cewa an Kama mutumin mai shekara 56 a duniiya mai suna Lawal Oyenuga a babban filin tashin jiragen sama na Murtala Mahammadu dake jihar Leges a kudancin Najeriya.

BabaFemi ya ce mutumin yayi yunkurin sanya hodar ibilis a cikin takalman sa ya shiga da su izuwa kasar Saudiya domin yin cinikayyar kwayoyi.
Sai dai Jami an su na hukumar ta NDLEA sun yi Nasarar Kama wanda ake zargin.
Daga karshe ya ce bayan kammala bincike za su mika wanda ake zargin zuwa kotu domin karbar hukunci.