Rundunar Yan sanadan Najeriya ta umarci dukanin kwamishinoninta na jihohi da su tura jami ai domin baiwa hukumar zabe INEC kariya.

Babban sufetan na kasa Usman Alkali Baba shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a ta bakin Mai maganar da yawun hukumar ta yan sanda Olumoyiwa Adejobi a jiya Lahadi.
A cewarsa za a gudanar za a ranar biyu ga watan fabarairu 2023.

Alakali Baba ya ce sun umarci dukanin kwamishinonin Yan sanda da su tura jami ai ofishin hukumar zabe ta kasa INEC domin bayar da kariya ga hukumar.

Sannan ya ci ga ba da cewa za garfanar da duk Wanda aka samu da tada tarzoma kalaman karya da tsattsauran ra ayin siyasa don yin haka barazana ne ga damakwaradiyya a Najeriya.
Sannan ya ce za a yi tsarin wanda za a samu damar lalubo hanayar da ya da ce baiwa INEC kariya yayin zabe ya Kara Karatowa.
Sannan Usman Alkali Baba ya ce kuma ya zama dole jama a su taya su gurin tabbatar da wannan aikin domin yan sanda kadai baza su iya aikin su kadai ba .