Gwamnan jihar Kebbi Atiku Bagudu ya amince a cire kashi 3% na albashin ma’aikatan gwamnatin jiharsa a karkashin shirin inshoran lafiya na Kebbi State (KECHEMA).

Wannan batu na amincewar gwamnan na zuwa ne daga bakin mai ba shi shawari kan harkokin yada labarai, Malam Yahaya Sarki a yau Talata a birnin Kebbi.
Alhaji Safiyanu Garba-Bena, mukaddashin shugaban ayyuka na jihar ya ce, amincewar gwamnan ya biyo bayan bukatar da kungiyar kwadago ta gabatar a jihar.

A tun farko, kungiyar ta kwadago ta nemi a cire kasho 3% daga albashin ma’aiakata tare da tura su ga asusun KECHEMA.

A cewar gwamnatin jihar, wannan zaftare albashi zai fara aiki ne daga wannan watan na Nuwamba don turawa ma’aikatar KECHEMA ta fara shirin samar da kayayyakin kiwon lafiya ga ma’aikatan gwamnati.