Babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ya umarci a tura jami’an tsaro domin dakile abin da ka iya faruwa a titin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Alkali Baba ya ba da wannan umarnin ne a daidai lokacin da hukumomin kasar nan ke shirin sake bude titin tare da ci gaba da daukar fasinjoji domin jigila a yankin.
Olumuyiwa Adejobi, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriyaa a jiya Lahadi ya bayana cewa, za a zagulo jami’an ne daga ‘yan sandan mobal, K-9, jami’an leken asiri da na sashen kunce bam da kuma na sashen jirgin kasa.

Manema labarai su ruwaito cewa, gwamanti ta amince a sake bude hanyar titin jirgin kasan Kaduna, kuma za a ci gaba da jigilar mutane daga ranar 5 ga watan Disamba, yau kenan.

Adejobi ya bayyana cewa, hukumar ‘yan sanda ta jima tana tattauna lamarin bude hanyar da hukumar jiragen kasan Najeriya (NRC) da ma sauran hukumomin tsaron da ke alaka da shi.
Ya kuma ambato IPG na cewa, hukumar na yin iyakar kokarinta don tabbatar da aminci da tsaro a titunan jiragen kasa a yankin da ma sauran yankunan kasar nan baki daya.
An sace mutane da yawa, wannan yasa ‘yan Najeriya ke ta cece-kuce kan yadda aka wulakanta fasinjojin jirgin.
Bayan haka ne gwamnati ta dakatar da jirgin tare da bayyana aikin ceto wadanda aka sace da kuma gano mafita ga tsaron hanyar.