Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a ranar Lahadi yayi kira ga takwaransa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da ya rage kudin makarantar jami’arsa dake Najeriya.

Atiku ne ya kafa jami’ar Amurka dake Najeriya a garin Yola dake jihar Adamawa.
Kwankwaso yayi wannan tsokacin ne yayin da yake amsa tambayoyi kan yadda za a inganta bangaren ilimi a wani taron da Arise TV ta gayyacesu tare da hadin guiwar cibiyar damokaradiyya da cigaba da jaridar Vanguard.

Ya ce dole ya yi godiya ga Wazirin Adamawa yana da jami’a wacce take da kyau sosai, abu daya da ya dace yayi kokarin yi shi ne ya yi kasa da kudin makarantar ta yadda magoya bayansa da ‘yan Najeriya masu yawa zasu iya shiga.

Kwankwaso ya kara da cewa, zai karfafa bangarori masu zaman kansu da su zuba hannayen jari a fannin ilimi tun daga firamare har zuwa jami’a yayin da yace komai dangane da ASUU dole ne ya zamo na gaskiya.
A yayin amsa tambayar, Atiku ya tsaya kan cewa ilimi yafi komai amfani cikin abubuwan da ya dace yara su samu ta yadda za a habaka cigaban kasa yayin da ya jaddada cewa a zuba kudi masu yawa a bangaren ilimi.
Atiku ya kara da bada misali kan yadda aka kirkiro UBEC yayin da yake mataimakin shugaban kasa wanda ya zama wajibi ga kowanne yaro ‘dan Najeriya da ya samu ilimin firamare zuwa karamar sakandare kyauta.