Hukumar kula da filayen noma ta kasa NALDA ta baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa kasar ba za ta fuskanci matsalar karancin abinci ba a shekara mai zuwa, duk kuwa da irin barnar da ambaliyar ruwa ta yi a filayen noma a fadin kasar.

Hukumar ta ce, ta samar da fili 500 na noman alkama wanda za’ayi noman rani a jihohin Adamawa, Yobe, Jigawa, Gombe da kuma Taraba domin samar da abinci.

Sakataren zartarwa na hukumar, Prince Paul Ikonne ne ya bayyana hakan inda yace an kawar da matsalar karancin abinci a shekara mai zuwa.

Ya kara da cewa hukumar a bana ta samar da injuna da kayan aikin noma a shiyyoyi shida na kasar dan habaka samar da abincin.

Ikonne ya bayyana haka ne a yayin wani taron manema labarai a jiya a Abuja inda ya bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shirya tsaf domin baje kolin nasarorin da NALDA ta samu cikin shekaru biyu da suka gabata.

A cewarsa, an samu gagarumin ci gaba wajen samawa matasa da mata aiyukan yi ta hanyar noma.

Ya kara da cewa shugaban kasa zai aza wani harsashi wanda hukumar zata yi aiki da manoma sama da 50,000 ban da kuma wanda zasu ci tallafin gajiyar filin kiwo .

NALDA ta dawo da aiyukanta sosai ne a kasan shugaban kasa Muhammadu Buhari, da nufin karfafa gwiwar matasan Najeriya da su rungumi harkar noma, da magance matsalar filaye.

Leave a Reply

%d bloggers like this: