Hukumar da ke kula da harkokin sadarwa a Najeriya – NCC ta yi gargaɗin cewa mutane za su iya shiga cikin haɗari idan suna shiga gasar bidiyo a shafin TikTok, inda ta ce za su iya faɗawa tarkon masu satar bayanan jama’a ta intanet.

Hakan na kunshe ne a cikin shawarar da NCC ta bayar inda ta ƙara da cewa masu kutse a intanet za su iya amfani da gasar ta TikTok wajen yaɗa manhajar satar bayanai ta intanet.
Ta ƙara da cewa za a iya satar sunan mutum da lambobinsa na sirri da harkokinsa na kuɗi ta hanyar amfani da dabaru na zamba a intanet.

TikTok na da matukar farin jini a Najeriya musamman a tsakanin matasa wadanda suke bajakolinsu nishadantarwa a shafin.

Shafin TikTok shi ne na tara a farin jini a tsakanin shafukan sada zumunta a Najeriya, sai dai hukumomin ƙasar ba su sanya wa shafin ido ba.