Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, a ranar Litinin ya umarci hukumar kula da gidajen gyaran hali ta sauyawa Dakaru mata waɗanda ba zasu iya kashe mutum ba, yanayin aiki.

Ministan ya ba da wannan umarnin ne a wurin taron bayyana Sabon tambari da Kaki da kuma kaddamar da gidajen ma’aikata, ICT da Motocin Operation a Hedkwatar hukumar dake Abuja.
Manema labarai sun rawaito cewa Jami’ai 25 waɗanda suka nuna kwazo da jajircewa wajen dakile harin ‘yan bindiga a gidan Yarin jihar Neja, sun sha yabo da kyauta daga wurin Ministan a wurin taron.

Da yake jinjina wa Jami’an, Aregbesola, ya nuna damuwarsa kan halayyar wasu jami’an gyaran hali, waɗanda ke tserewa idan ‘yan ta’adda sun kawo hari.

A cewarsa, Gidan yari ya zama wuri mai haɗari a yanzu kuma ya kamata Dakaru su yi harbi tare da sheƙe kowaye ya yi yunkurin kai hari wuraren.