Wasu daga cikin mayakan Boko Haram sun hallaka akalla matan mayakan ISWAP 33 a dajin Sambisa domin daukar fansan kisan Malam Abubakar (Munzir) da wasu mayaka 15 da aka halaka a wani artabu da aka yi.

Tun ranar 3 ga watan Disamba, wani babban ‘dan Boko Haram dake kula da tsaunin Mandara, Ali Ngulde, ya jagoranci daruruwan mayaka dauke da makamai domin yakar ‘yan ta’addan ISWAP dake dajin Sambisa.
Farmakin ya fara ne bayan an yi kokarin yin sasanci tsakanin kungiyar Boko Haram da ta ISWAP kan cewa su shirya yin mubaya’a ga shugabannin IS/ISWAP.

Bayan wannan arangamar, ‘yan Boko Haram sun kwace motoci kirar Hilux guda hudu daga abokan hamayyarsu kuma suka kone su.

Wata majiya tace jim kadan bayan wannan nasarar, Boko Haram ta sake shirya mayaka daga sansanin Abu Iklima dake Gaizuwa, Gabchari, Mantari da Mallam Masari domin su kai hari kan ‘yan ISWAP dake Ukuba, Arra da Sabil Huda da Farisu inda aka halaka mayaka