Hukumar kula da yaki da rashawa ta ICPC a Najeriya ta ce ta kama fitaccen mawakin nan mai suna Oladipo Oyebanj, wanda aka fi sani da D’Banj kan wani bincike da take yi wanda ya shafi kudaden shirin Npower.

Wata sanarwa da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet ta ce ta kama D’Banj ne saboda ya ki martaba gayyatar da hukumar ta yi masa game da batun.
Sanarwar ta ce ta gayyaci kimanin mutum 10 a cikin watannin da suka gabata, kuma tuni ta sake su bayan kamala bincike.

Sai dai a cewar hukumar ta rike mawakin ne bayan da ya kai kansa hukumar a Abuja saboda kin martaba gayyatar da ta yi masa.

Hukumar ICPC ta ce yanzu haka na tsare a ofishinta kuma yana bada cikakken hadin kai kan tuhumar da ake yi masa.
Ta kuma ce za ta tabbatar an hukunta wanda aka kama da laifi hade da hade da bankunan da suka taimaka wajen yin badakalar