Wata  kotu a kasar Argentina ta yanke wa mataimakiyar shugaban kasar Argentina, Cristina Fernandez, hukuncin daurin shekara shida.

Hukuncin kotun ya kuma haramta wa Fernendez rike mukamin gwamnati har zuwa karshen rayuwarta.

Kotun ta yanke mata wannan hukunci ne a zamanta na jiya bayan da ta same ta da laifin yin ruf da ciki kan Dala miliyan daya da aka ware don aiwatar da ayyukan gwamnati.

Sai dai kotun ta wanke mataimakiyar shugaban daga zargin mallakar haramtaccen kamfani, wanda idan da hakan ya tabbata hukuncin daurin shekara 12 ne a gidan yari.

Wannan shi ne karo na farko da irin hakan ta faru a tarihin kasar ta Argentina.

Sai dai wannan hukunci ba zai tabbata ba har sai bayan Fernandez ta daukaka kara , kuma ya zamana ba ta yi nasara ba.

Hakan nan ba zai yiwu a kama ta ba saboda rigara kariya da take sanye da ita albarkacin mulki.

Tuni dai magoya bayan mataimakiyar shugaban kasar na Argentina suka sha alwashin haifar da cikas ga harkokin kasar ta hanyar zanga zanga.

Leave a Reply

%d bloggers like this: