Dan takarar Sanatan kano ta tsakiya a jam’iyyar APC Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya ce babu wata barazana ko tsoratarwa da zata hana shi jajirce wa wajen yakin neman zaben sa.

Zaura wanda ke fuskantar tuhume-tuhume a gaban kotu da hukumar yakin da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC keyi masa.
Ya bayyana haka ne a birnin kano lokacin da yake zantawa da manema labarai kan shirinsa na takarar sanata a lokacin zabe da kuma bayan zabe.

Zaura ya ce shima daga cikin masu karamin karfi ya taso don haka yasan kalubalen mutanan yankinsa,
Ya kara da cewa babu abinda zai iya tsayar dashi ko tsorata shi wajen kasancewar sa tare da jamma’arsa domin taimakwa rayuwarsu.

Dan katarar ya bayyana cewa babu wata barazana ko matsin lamba da zai sa ya janye takararsa a babban zabe na shekarar 2023.