Yan bindiga sun sace ilahirin iyalan wani dan majalisar dokokin jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Maharan sun sace iyalan Aminu Yusuf Ardo ne ranar Alhamis da daddare a kauyensu Jangebe.
Shedun gani da ido sun ce ‘yan bindigar sun dirar wa gidansa da talatainin dare inda suka sace matarsa da ‘ya’yansa hudu, bayanai sun tabbatar da cewa dan majalisar ba ya gida a lokacin da lamarin ya faru.

Aminu Yusuf Ardo dai yana wakiltar mazabar Talata-Mafara ta Kudu a majalisar dokokin jihar Zamfara.

Kazalika ‘yan bindigar sun sace akalla mutum takwas ,wanda yawancinsu makwabtan dan majalisar dokokin ne a cewar mazauna kauyen.
Wani mutum da mahaifinsa yana daya daga cikin wadanda aka sace ya shaida wa manema labarai cewa sun yi matukar kaduwa, sannan kawo yanzu ‘yan bindigar sake su bayan an tattauna da ‘yan bindigar.
Zamfara dai na cikin jihohin da ke fama da matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa a Najeriya.
