Ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya sake jaddada cewa tun daga ranar da ya zama shugaban ƙasa a 2023 zai fara sauya wa Najeriya fasali.

Ya ce zai yi amfani da yarjejeniyar sa ta sauya fasalin Najeriya domin ya kawo ƙarshen matsalar tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar nan ke fama da ita.
Ya ce daga lokacin da aka gama rantsar da shi zai fara aiwatar da ayyukan raya ƙasa ta hanyar sake fasalin Najeriya.

Yace babban muradin su shi ne su tabbatar sun kawar da dukkan matsalolin rashin tsaro, rarrabuwar kawuna, kawar da danne haƙƙin tallalin arzikin ja’am’a da samar da aikin yi ga matasa.

Yace yana ɗaukar wa ‘yan kasa alƙawarin cewa tun daga ranar da aka naɗa shi shugaba idan ya yi nasara a zaɓen 2023, zan aiwatar da su.
Daga nan sai ya roƙi al’ummar jihar Osun su jefa masa ƙuri’un su, domin ya cimma burin sa na ceto Najeriya daga mawuyacin halin da ya ce jam’iyyar APC mulkin Ta jefa ƙasar.
Atiku yace baza su kunyata al’umma ba, kuma ba za su ci amanar al’umma ba kamar yadda APC tayi Saboda su suna da ƙwarewa da irin gogewar da Najeriya ke matuƙar buƙata A halin yanzu.
Gwamna Ademola Adeleke, wanda aka rantsar ya bayyana Atiku Abubakar a matsayin gogagge kuma mai ƙwarewar da zai iya ceto Najeriya, har ya magance matsaloli da ƙalubalen da su ka dabaibaye ƙasar.