Shugaba Muhammadu Buhari ya ce yana kyautata zaton cewa jam’iyyar APC ne za ta lashe dukkan kujeru cikin adalci a zaben shekarar 2023.

Shugaban kasar kuma ya bawa jam’iyyar ta APC da yan takararta tabbacin cewa a shirye ya ke ya yi wa dan takarar shugaban kasa da sauran yan takarar kamfen ‘da kuzarinsa da niyya mai kyau.

Wannan tabbacin a cewar sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a bangaren watsa labarai, Mallam Garba Shehu, an yi ta ne don kore damuwar da wasu ke yi na cewa shugaban kasar baya zuwa kamfen tun bayan kadamarwa a jihar Plateau.

Sanarwar ta ce duk da cewa shugaban kasar bai yi watsi da harkokin jam’iyya ba, ba zai yi wu kuma ya manta da ayyukansa ba a matsayin shugaban kasa.

Da ya ke magana da yan Najeriya a Washington DC yayin ziyararsa Amurka, Buhari ya jadada cewa a shirya yake kowane lokaci ya fita yin kamfen don nasarar jam’iyyarsa a zaben 2023.

Sun kasance abin ban sha’awa kuma da cikaken karfinsu,’ idan aka kwatanta da abokan hammayar da bisa alamu ke kokarin bin sahun su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: