Shugaban hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (NSCDC), Ahmed Abubakar Audi, ya bayyana cewa akwai wata kungiya mai hatsarin gaske a Najeriya da ke haddasa rikici.

Audi ya bayyana hakan ne yayin bude taron kwamandojin rundunar na shekarar 2022 tare da kwamandojin jihohi a hedkwatar NSCDC a yau Laraba a Abuja.
Audi ya ce an gano kungiyar ne sakamakon bayanan sirri da hukumar ta samu.

Shugaban na NSCDC yayin da ya ke zaburar da kwamandojin hukumar ya ce.

Ya zaburar da kwamandojin yankuna da jihohi su rika aiki tare da sauran hukumomin tsaro don tabbatar sun kare kayan gwamnati a jihohinsu yayin da ke magana kan hare-haren da ake kaiwa INEC.
Ya bukaci su mayar da hankali kan tattaro bayanan sirri, yana mai cewa ‘kare afkuwar laifi ya fi sauki fiye da magance shi’. Shugaban na NSCDC ya bukaci kwamandojin yankuna su saka idanu kan tafiyar da jami’ansu, kuma zai rika sauraron bayanai na abin da ke tafiya a karkashin yankinsu duk minti-minti.