Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun Litinin 26 ga Disamba da Talata 27 ga Disamban da mu ke ciki a matsayin ranar hutu ga ma’aikata don hutun kirsimeti.

Haka kuma gwamnatin ta zaɓi ranar Litinin 2 ga watan Janairun sabuwar shekara 2023 a matsayin ranar hutu domin murnar zagayowar sabuwar shekara.
Sanarwar da ta fito daga ofishin minsitan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola, an bukaci mabiya addinin kirista da su yi amfani da damar wajen yi wa ƙasa addu’a.

Sannan sanarwar ta bukaci mabiya addinin da su yi koyi da koyarwar littafin Bible ta hanyar kyautatawa da taimako.
