Rundunar ‘yan sandan Jihar Imo ta sallami wasu jami’anta bakwai daga bakin aiki sakamakon yiwa mutane kwacen kudade.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Muhammad Barde ya ce jami’an ‘yan sandan suna tare mutane ne daga bisani su tafi da su wasu gurare na daban domin su karbe musu kudaden su.
Barde ya kara da cewa asirin jami’anna su ya tonune sakamakon korafe-korafe da al’umar Jihar su ka gabatar wa rundunar.

Muhammad Barde ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Owerri babban birnin Jihar ga manema labarai.

Kwamishinan ya kara da cewa jami’an suna amfani ne da na’urar cire kudi ta POS inda su ke karbar katin cirar kudin mutanen su cire.
Barde ya ce bayan samun bayanin ta’asar da jami’an yan sandan su ke yi su ka dauki matakin korarsu daga bakin aiki.