Rundunar tsaro ta Najeriya ta tabbatar da cewa ta fara bincike akan zargin hallaka fararen hula a yayin wani lugudan wuta da jirgin yakin jami’an tsaron soji ya kai wa ‘yan bindiga a Jihar Zamfara.

Daraktan yada labaran hedkwatar tsaron Janar Musa Dan-madami ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhami.
Dan-madami ya ce hedkwatar ta tsaro ta kafa wani kwamiti da zai yi bincike domin gano hakikanin abinda ya faru tare da tantance adadin mutanen da su ka rasa rayukan su.

Musa Dan-madami ya bayyana cewa a yayin harin jirgin yakin sun hallaka ‘yan bindiga da dama.

Kazalika Janar Dan-madami ya kara da cewa rahotanni daga Jihar ta Zamfara sun bayyana cewa mutane 60 ne su ka rasa rayukansu a harin.
Daraktan ya ce kawo yanzu babu wani rahoto da gwamnatin Jihar ta fitar na adadin mutanen da su ka rasa rayukan su a yayin harin da jirkin yakin ya kaiwa yan bindiga a Jihar.