Wasu mahara a Jihar Kaduna sun yi garkuwa da mutane 37 a yayin wasu hare-hare da su ka kai wasu kauyuka a Jihar.

Sarkin Azara Mustapha Ibrahim ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis.

Sarkin na Azara ya ce ‘yan bindigan sun shiga kauyen ne a cikin dare inda su ka kwashe mutane goma ciki harda masu shayar da yara.

Maharan sun yi garkuwa da mutanen ne cikin kwanaki uku a kauyukan Janjala Azara da Kadara da ke kananan hukumomi Kagargo da Kachiya duk da ke Jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa mafiya yawan wadanda yan bindigan su ka sace mata ne da kananan yara.

A harin na ‘yan ta’addan sun hallaka wani tsohon soja tare da dansa a kauyan Katambi da ke kusa da kauyan Kateri.

Sarkin na Azara ya ce kafin shaidawa jami’an tsaron sojin da ke sintiri a yankin ‘yan bindigan sun tsere.

Leave a Reply

%d bloggers like this: