Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El’Rufa’i ya bai wa Abdullahi Daniya sandan sarauta a matsayin sarkin Jere na 11.

Bikin rantsuwar ya gudana ne a ranar Juma’a a filin wasa na garin Jere da ke Jihar.

A yayin bikin bayar da sandar gwamnan Jihar ya mika jinjinawa al’ummar garin na Jere sakamakon hadin kan da su ke bayar wa domin ganin tsaro ya tabbata a yankin.

El’Rufa’i ya kara da cewa gwamnatinsa ta na iya kokarin ta domin tabbatar da tsaro da dukiyoyin al’umma a dukkan fadin Jihar.

Gwamna El’Rufa’i yayi kira ga al’umma Jihar da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro hadin kai domin kawo karshen ‘yan ta’adda a Jihar baki daya.

Sannan ya kuma bukaci mutanen da ke masarautar ta jere da su yiwa sabon sarkin mubayu a.

A yayin bikin manyan mutane da dama ne su ka halarci bikin rantsuwar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: