Jami’an rundunar sojin Najeriya sun hallaka ‘yan ta’adda takwas a yankin Chikun da birnin gwari da ke Jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Samuel Aruwan ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Aruwan ya ce dakarun rundunar hadin giwa na Operation Forest Sanity ne su ka samu nasarar hallaka ‘yan bindigan.

Kwamishinan ya kara da cewa bayan hallaka ‘yan bindigan jami’an sun kwato babura guda hudu tare da wayoyin hannu.

Aruwan ya ce bayan hallaka takwas din jami’an su ka sake kwato babura biyu daga hannun wasu yan bindigan.
Kazalika ya kuma ce jami’an sun sake hallaka wasu ‘yan bingida biyu a yankin sabon birni da maidaro kuma dogon Dawa duk da ke Jihar.
Sannan jami’an sun kwato bindiga kirar AK47 tare da harsasai daga hannun su.