Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga hukumomin tsaron ƙasar da za su yi aiki da hukumar zaɓen ƙasar a lokacin zaɓukan 2023 da ke tafe da su kasance ‘yan ba-ruwanmu, tare da nuna ƙwarewar aiki.

Sannan kuma su nesanta kansu daga duk abubuwan da za su kawo matsala ga ayyukansu a yayin zaben da kuma bayan kammala zaben.

Shugaba Buhari ya bayar da umarni ga jami’an ne ranar Laraba a lokacin bikin ƙaddamar da rukunin gidajen jami’an hukumar tattara bayanan sirri a unguwar Idu da ke babban birnin tarayyar Abuja.

Buhari ya umarci hukumomin tsaron da su tabbatar da cewa sun kula da ayyukan rarrabawa tare da lura da muhimman kayayyakin zaɓe cikin nuna ƙwarewar aiki kamar yadda yake kunshe cikin dokokin hukumomin tsaron.

Leave a Reply

%d bloggers like this: