Akalla mutane bakwai ne su ka raya rayukan su a wani hadarin mota da ya afku a Kauyen Gunu da ke karamar hukumar Munya ta Jihar Neja.

Kwamanda a hukumar kiyaye afkuwar hadurra ta kasa FRSC reshen Jihar Kumar Tsukwam shine ya tabbatar da faruwal lamarin.

Tsukwam ya ce lamarin ya farune a daren jiya Talata a tsakanin wasu motoci guda biyu kirar Toyota Camry da wata Bass.

Kwamandan ya kara da cewa a yayin hadarin mutane biyar sun jikkata yayin da mutane bakwai kuma su ka rasa rayukan su.

Kumar ya bayyana cewa bayan faruwal lamarin sun samu kudi naira 36,200 da buhun doya daya kyamara kirar Nakon Batiran waya guda biyu karamar Jaka da kuma katunan daurin aure.

Kazalika Tsukwam ya ce wadanda lamarin ya rutsa da su an aike da su Asibiti domin kula da lafiyar su tare da kai wadanda su ka rasa rayukan su dakin adana gawarwaki da ke Asibin garin Minna.

Sannan ya ce sun kai motocin da su ka yi hadarin Ofishin ‘yan sanda da ke garin Munya domin fadada bincike.

Kwamandan ya kuma yi kira ga matuka ababan hawan da su gujewa gudun wuce sa’a domin kiyaye afkuwar hakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: