Kasar Qatar za  ta kyautar da manyan motocin daukar fasinja da aka yi amfani da su a gasar kofin duniya ga kasar Lebanon domin taimaka wa harkokin sufuri a kasar.

Hakan na zuwa ne bayan da hukumomin kasar Qatar suka bayyana aniyarsu ta kyautar da wasu kayayyakin da ta yi amfani da su a lokacin gasar kofin duniya ga wasu kasashe masu tasowa.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa firaminastan kasar ta Lebanon Najib Mikati ya tattauna batun da jamian kasar Qatar bayan kammalla gasar kofin Duniya.

Cikin abubuwan da Qatar din ta ce za ta kyautar har da manyan filayen wasanni da aka yi amfani da su a lokacin gasar, da kujerun da ke filayen wasan, baya ga manyan motoci guda dubu daya da aka yi amfani da su wajen yin zirga zirga da yan kallo kyauta a lokacin gasar.

Kasar Qatar dai ita ce ta karbi gasar kofin duniya a wannan shekara bta 2022 wanda aka kammala a ranar 18 ga wata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: