Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya kambama kwamandan dogaran fadarsa da aka yi wa karin girma, Manjo-Janar Muhammad Usman, inda ya siffantasa a matsayin jami’in tsaro na daban wanda ke bautarwa kasa cikin kaimi.

Shugaban kasar, a gaban Shugaban jami’an soji, Lt. Janar Faruk Yahaya da matar dogarin, Pharm (Dr) Rakiya Usman, ya kambama jami’in da ya samu karin girma zuwa matakin Manjo-janar.

Yayin jawabi jim kadan bayan bikin karin girman a fadar shugaban kasa, shugaban kasar yayi tuni game da irin hidimtamawa rundunar sojin da jami’in yayi, inda ya siffanta janar Usman a matsayin jami’i mai matukar sa’a duba da yadda ya kai kololuwa a matakin soji ba tare da sarewa ba.

Channels TV ta rahoto cewa, ya jinjinawa janar Usman bisa ga juriya, biyayya, hakuri da kokarinsa.

Shugaban kasar ya ce zai bada umarni kan aikin da Manjo-Janar zai yi a gaba, duba da yadda shima yake kokarin barin madafun iko, sannan kamar yadda ya saba fadi, zai koma wuri mai nisa daga Abuja.

Haka zalika, Shugaban kasa Buhari ya jinjinawa iyalan jami’in sojan bisa hakurinsu wajen jurewa da aikinsa mai matukar wahala da yake aiwatarwa ba tare da sarewa ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: