Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta bayyana cewa a cikin shekarar 2022 da mu ke bankwana da ita ta hallaka ‘yan bindiga 21 tare da kama wasu da dama.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Yekini Ayoku ne ya bayyana hakan a rahotan karshen shekara da rundunar ta fitar.
Ayoku ya ce jami’anna su sun kuma kubtar da mutane 206 daga hannun ‘yan bindigan da su ka yi garkuwa da su.

Kwamishinan ya kara da cewa akalla dabbobi 1,446 da ‘yan bindigan suka sace a sassan Jihar jami’an su ka ceto.

Yekini ya ce kawo yanzu jami’an sun kuma kwato bindigogi 49 alburusai 1,359 babura 17 buhunan 15 na wani ganye wanda ake zargi na tabar wiwi ne daga hannun Maharan da su ka addabi Jihar.
Kazalika Kwamishinan ya bayyana cewa akalla mutane 780 jami’an su ka kama sakamakon aikata laifuka daban-daban a fadin Jihar.
Yekini ya ce rundunar ta gurfanar da akalla mahara 116 a gaban kotu domin fuskantar hukunci.