Majalisar dattawan Najeriya ta roki babban banki na CBN ya tsawaita wa’adin da ya bada na canza tsofaffin kudi zuwa tsakiyar shekarar badi.

 

An rahoto cewa majalisar dattawan ta na so lokacin da za a daina karbar tsofaffin kudi ya koma 31 ga watan Yuni maimakon karshen Junairun 2023.

 

A zaman da aka yi na ranar Laraba, 28 ga watan Disamba 2022 a majalisar dattawan kasar, an bijiro da maganar canjin manyan kudin da CBN ya yi.

 

Sanata Ali Ndume mai wakiltar Kudancin jihar Borno ya roki a kara lokacin da aka bada domin gudun a jefa mutanen Najeriya cikin halin ha’ula’i.

 

An rahoto Ndume ya ce tuni mutane sun fara fama da bin dogayen layi a bankuna, su na neman hanyar da za a ba su sababbin Nairorin da aka buga.

 

‘Dan majalisar ya ce da zarar an fara raba sababbin kudin da aka fitar, ‘yan kasuwa za su rika gujewa tsofaffin kudin da ake shirin daina aiki da su.

 

Bugu da kari, Sanatan na APC ya ce samun sababbin kudin yana wahala domin CBN ya yanke adadin kudin da mutum ko kamfani zai karba a rana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: