Wasu da ake zargin bata gari ne sun sanya abin fashewa a fadar Sarkin Okene da ke yankin na Okene a Jihar Kogi.

Abun fashewar ya tashi ne a safiyar yau Alhamis a lokacin da ake sa ran shugaban kasa Muhammad Buhari zai halarci Jihar domin kaddamar da wasu ayyuka.
Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa a yayin fashwar abun mutane uku ne su ka rasa rayukansu.

Bayan faruwal lamarin jami’an ‘yan sanda da ke aikin kwance bama-bamai na Jihar sun halarci gurin da lamarin ya faru.

Kawo yanzu ba a san musabbabin sanya abin fashewar ba.
rundunar ‘yan sandan Jihar tuni na aike da jami’an tsaron ta yankin domin tabbatar da tsaro a yankin da lamarin ya faru.