Dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a jihar Katsina, Dr. Dikko Umar Radda, ya bayyana cewa zai yi amfani da matasa don yakar yan bindiga idan ya zama gwamnan jihar a 2023.

Dikko ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga dandazon jama’ar da suka fito don tarbar tawagarsa a yayin rangadin yakin neman zabensa a Batsari, daya daga cikin kananan hukumomin da ke fama da aikin ta’addanci a jihar.
A cewar mai neman zama gwamnan, za a horar da matasa, a basu kayan aiki sannan a tura su don taimakawa jami’an tsaro a yaki da yan bindiga a jihar.

Ya kuma ce wannan hanyar za a yi amfani da shi wajen yakar miyagu da kare yankunansu daga mahara.

Dikko ya kuma yi alkawarin kawo karshen shanya rogo da ake yi a kan hanya a yankin ta hanyar samar da injinan da za su yi hakan cikin sauki, rahoton Independent.
Tsohon shugaban na SMEDAN ya kuma bayyana cewa takardar manufarsa ta tanadi hanyoyin bunkasa harkar noma ta hanyar samar da injinan noma wanda zai kawo riba ga manoma a yankin.