Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya yi kira ga al’ummar yankin Karamar Hukumar Alkaleri da su dauki makamai don kare kansu daga ’yan ta’adda.

Bala ya yi wannan kira ne ranar Alhamis a lokacin da ya ziyarci fadar Sarkin Yelwan Duguri, Alhaji Adamu Mohammed Duguri, yayin ziyarar da kai kauyukan Rimi da Gwana da Yalwan Dugari.

Ya ziyarci kauyukan ne domin jajanta musu kan harin da ’yan bindiga suka kai musu a baya-bayan nan.

Gwamnan ya ce, ba za a bari ta’addancin ya ci gaba da aukuwa ba, dole a dauki matakin dakatar da shi ta kowane hali.

A cewarsa, ya bai wa rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro umarnin su kula duk wani dan bindiga da aka kama saboda ba zai yiwu su ci gaba da asarar mutanensu haka kawai ba.

Idan za a iya tunawa abaya rawaito ’yan bindiga suka kashe mutum 17 a harin da suka kai kauyen Rimi da ke jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: