Akalla mutane 17 ne ka rasa rayukan su yayin 15 jikkata a gurin rububin dibar sabbin kudade a unguwar Hausawa da ke layin Bagobiri a garin Kalaba.

Wani shaidan gani da ido ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata da ta gabata a lokacin da ake bikin al’ada a yankin inda wani mutum yazo ya watsa kudaden wanda hakan ya saya mutane su ke rububin dibar kudin.
Shaidan ya bayyana cewa bayan faruwal lamarin aka miki wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa Asibiti inda gwamnatin Jihar ta dauki nauyin su.

Daga bisani kuma gwamnan Jihar ya aike da tawaga ta musamman karkashin jagoran kwamishinan yada labarai na Jihar domin jajantawa wadanda lamarin ya faru da su.

Kwamishinan ya ce za su yi bincike domin gano mutunen da ya haddasa lamarin.