Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan kasafin kudin 2023 a ranar Talata, 3 ga watan Janairu.

Tun farko majalisar dokokin kasar ta aiwatar da kasafin kudin da ya kai jimillar naira tiriliyan 21.83.


Shugaban kasar ya rattaba hannu a takardar a fadar shugaban kasa a gaban shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan; Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da sauran mambobin majalisar dokokin tarayya.
Kakakin shugaban kasa Femi Adesina, ya rubuta a wata sanarwa da ya saki.
“Da yake jawabi a wajen sanya hannu a kasafin kudi na takwas kuma na karshe a wannan gwamnai, shugaban kasar ya ce jimillar kudaden da za a kashe ya kama naira tiriliyan 21.83, Karin naira tiriliyan 1.32 kan kasafin kudin baya na naira tiriliyan 20.51.”