Wata gobara ta kone dakin gwaje-gwaje da ke Asibitin kwararru na garin Jos a Jihar Filato.

Lamarin ya faru ne a daren ranar Talata inda gobarar ta yi asarar kadarorin miliyoyin nairori.
A yayin tashin gobarar ba a samu a sarar rayuka ba,inda wutar ta cinye iya kacin dakin gwaje-gwajen.

Mai magana da yawun Asibitin Talatu Angi ta tabbatar da faruwal lamarin.

Talatu ta ce wutar ba ta kama sauran dakunan da ke cikin Asibtin ba.
Kakakin ta kara da cewa daga cikin kayayyakin da su ka kone sun hada da kayan aikin ofis da sauran wasu kayayyaki miliyoyin nairori.
Talatu ta ce jami’an hukumar kashe gobara ta Jihar sun samu nasarar kashe wutar.