[contact-form][contact-field label=”Name” type=”name” required=”true” /][contact-field label=”Email” type=”email” required=”true” /][contact-field label=”Website” type=”url” /][contact-field label=”Message” type=”textarea” /][/contact-form]

Hukumomi a Jihar Kebbi sun samu zarafin gano gawarwakin manoma 16 wadanda hadarin jirgin ruwa ya rutsa da su a cikin karamar hukumar Koko Besse da ke Jihar Kebbi.

Hukumomin sun ce kawo yanzu su na ci gaba da neman ragowar gawarwaki shida daga cikin mutanen da su ka bace.

Bayan faruwal lamarin gwamnan Jihar Atiku Bagudu da ministan shari’a Abubakar Malami sun kai ziyarar jaje yankin da lamarin ya faru.

A yayin ziyarar gwamnan ya nuna alhinin sa ga ‘yan uwan wadanda lamarin ya rutsa da su tare da addu’a neman wa matatan gafara.

Gwamna Bagudu ya ja kunnen matuka jiragen da su kaucewa tafiyar dare tare da yin dodin da ya wuce kima da kuma daukar matakan kariya a yayin tafiyar.

Bagudu ya kuma jinjinawa wadanda su kq gudanar da aikin ceto mutanen da su ka nitse a cikin ruwan.

Anasa bangaren shugaban karamar hukumar Alhaji Yahya Bello ya mika godiyar sa ga gwamnan bisa ziyarar jaje da ya kaiwa mutanen yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: