Dakarun Operation hadin kai na bataliya 195 sashi na daya hadin gwiwa da jami’an tsaron sa-kai sun hallaka mayakan boko haram hudu a yankin Mafa da ke Jihar Borno.

Dakarun sun hallaka mayakan ne a sansanonin su da ke yankin Karkut da Kashode tun a ranar biyar ga watan Disamban shekarar da ta gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an sun samu nasarar ne sakamakon bayanan sirri da su ka samu.

A yayin harin hadin gwiwar jami’an sun yi musayar wuta da mayakan na boko haram wanda hakan yayi sanadiyyar hallaka mayaka hudu da dama kuma su ka jikkata sauran su ka tsere.

Jami’an sun kuma tarwatsa maboyar mayakan shida daga bisa kuma sa ka gano abubuwan fashewa makamai da kuma wayoyin hannun.

Dakarun sun kuma sake bincike yankin su ka tashi sauran sansanonin mayakan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: