Kungiyar Kiristocin Najeriya(CAN) ta yi kira ga matasa a kan kada su yarda su siyar da kuri’unsu a babban zabe mai zuwa.

Babban sakataren matasan CAN reshen Abuja, Joseph Daramola, ne ya yi kiran a yayin wani gagarumin gangamin matasa a Abuja a ranar Lahadi, 8 ga watan Janairu.


CAN ya baiwa matasa aiki gabannin zaben shugaban kasa na 2023
Ya bayyana cewa an gasawa matasan Najeriya aya a hannu don haka, sun matsu su yi abun da ya dace a yayin da ake tsaka da fargabar rashin sanin me gobe za ta haifar.
Damarola ya bayyana cewa kowace jam’iyyar siyasa na da yancin zabar duk wanda suke so a matsayin abokin takara, addini guda ko akasin haka, rahoton The Guardian.