Hukumar tsaro ta Civil Defence (NSCDC) ta tabbatar da harbe jami’anta bakwai da wasu ’yan bijilanti biyar har lahira da ’yan bindiga suka yi a wurin hakar ma’adanai na Kuringa da ke Birnin Gwari a Jihar Kaduna.

Kakakin NSCDC, Olusola Odumosu ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Talata a Abuja, inda ya ce lamarin ya faru ne ranar Litinin da karfe 10:00 na safe.

Haka kuma ya ce jami’in hukumar guda daya ya tsira da munanan raunuka, kuma yana kwance a asibiti yana karbar magani gawarwakinsu kuma an ajiye su a mutuwaren Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna.

Haka-Zalika suma maharan sun rasa mutum daya daga cikin tawagar su yayin artabu tsakaninsu da jami’an tsaron.

Ya ce bayanai na nuna cewa sai da maharan suka kwashe makaman jami’an tsaron kafin su hallaka su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: